Ficewar Abaribe daga jam’iyyar PDP babban koma bay ne – Shehu Sani
Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewar al’umma kuma tsohon dan majalisa dattawan Najeriya, Shehu Sani, ya bayyana cewa ficewar Sanata Enyinnaya Abaribe daga jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP, a matsayin koma baya ga jam’iyyar.
A baya Arewa Post Hausa ta ruwaito cewa Abaribe, wanda ya fice daga PDP ranar Juma’a, shi ma yayi murabus a matsayin shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar.
Da yake mayar da martani kan sauya shekar Sanata Abaribe, Shehu Shani a shafin shi na Twitter ya rubuta cewa, “Rahoton ficewar Sanata Enyinnaya Abaribe daga PDP babban koma baya ne ga yan adawa.
“Fitaccen dan majalisa ne kuma mai karfin fada a ji wajen tabbatar da adalci da gaskiya da rikon amana. Abin takaici ne yadda ba a iya magance matsalar Abia cikin ruwan sanyi ba.”