Labarai

Direbobin Motocin Dangote 3 Sun Mutu A Wani Hatsari A Kogi

Ma’aikatan kamfanin simintin Dangote uku sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 5:45 na yamma a kusa da hanyar Zariagi Obajana a jihar Kogi.

Wadanda suka mutu a cewar wata majiya daga kamfanin sun hada da Victoria, Beatrice, da Aliyu.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, hatsarin ya rutsa da motoci hudu: wata babbar mota, wata motar bas ta alfarma, Toyota da Peugeot 406.

Shedun gani da ido sun bayyana cewa da dama sun jikkata a hatsarin kuma a halin yanzu suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunan shi ba.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kogi, Stephen Dawulung, ya tabbatarwa jaridar DAILY POST faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Masu Alaƙa