Wasanni
Dan Wasan Faransa N’Golo Kante Ba Zai Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ba bayan Tiyatar Da Aka Yi Masa

Dan wasan tsakiya na Faransa N’Golo Kante ba zai buga gasar cin kofin duniya ba bayan da Chelsea ta ce ana sa ran zai yi jinyar watanni hudu bayan tiyatar da yayi a kafar shi.
“Dan wasan tsakiya ya ziyarci kwararre tare da sashen kula da lafiya na kulob din don gano hanyoyin da za a bi don gyaran lafiyar shi kuma an amince da N’Golo a yi masa tiyata don gyara barnar,” in ji kulob na Ingila a ranar Talata.
Dan wasan tsakiya na Faransa wanda ya lashe kofin duniya na 2018 ya koma Chelsea a 2016 daga Leicester City kuma tun daga lokacin ya kasance wani muhimmin bangare na Blues.