Chadi Ta Ayyana Dokar Ta Ɓaci Bayan Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Mutane Sama Da Miliyan Ɗaya

Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya sanar da kafa dokar ta-baci da yammacin jiya Laraba, inda ya bayyana alhini game da asarar rayuka da na dukiya da ambaliyar ruwa ta haddasa a kasar.
Ambaliyar ruwa mai karfin gaske a kasar da ke tsakiyar Afirka tana shafar yankuna 636 a yankuna 18 daga cikin 23 na kasar, wato sama da mutane miliyan daya, lamarin da yasa haddasa dubun dubatar yan gudun hijira tare da lalata dubban gonakin noma a cewar Deby.
Ya sanar da kafa dokar ta-baci don shawo kan lamarin, da kuma shawo kan wannan bala’in, wanda yace ya samo asali ne sakamakon sauyin yanayi kuma daya daga cikin mafi muni da yankin ya fuskanta cikin shekaru.
“Halin da ake ciki na kara dagula al’amura,” in ji shi, inda ya koka da ababen more rayuwa da ba a tsara su ba bisa la’akari da bayanan yanayi da na ruwa a halin yanzu ba.
Deby ya kuma yi gargadin cewa barnar fiye da yadda aka gani za ta iya faruwa yayin da ambaliyar ruwan ta ja baya a kudancin kasar.
Yankunan da suka fi fallasa su ne birnin N’Djamena, babban birnin kasar, da kewaye, in ji shi.