Canada Ta Hana Ayyukan Kamfanonin Sadarwa Na kasar China

Kasar Canada ta ce za ta dauki matakin haramtawa Huawei da ZTE samar da sabis na 5G a kasar, a wani mataki na baya-bayan nan da wata kawancen Amurka ta dauka na yiwa kamfanonin kera kayayyakin sadarwa na kasar Sin hari.
An dade ana sa ran Kanada za ta dauki irin wannan matakin, inda a yanzu ta shiga sahun manyan kasashe biyar da ke kiran kansu “Ido biyar” da ke raba bayanai da suka hada da Amurka, UK, Australia da New Zealand.
Yanzu duk wani kamfani na kasar Canada da ya riga ya sanya na’urar da kamfanin Huawei ko ZTE na kasar Sin ya kera, za a bukaci ya cire ta.
Haɗin Intanet na 5G yana da inganci, sauri, kamar walƙiya, kuma ya ƙunshi ƙarin bayanai fiye da 4G.
Kafin wannan matakin, Kanada ta ce a cikin wata sanarwa a watan Satumba na 2018 cewa “za ta yi la’akari da yiwuwar barazanar da amfani da na’urorin Huawei ko ZTE da China ke bayarwa.”
Herman da tsohon mai ba Amurka shawara kan tsaro Robert C. O’Brien, suna rubuce-rubuce a The Hill, a cikin Disamba 2021, kasashe 8 ne kawai suka yarda su dakatar da kayan aikin Huawei na 5G, amma sama da ƙasashe 90 sun yi rajista da Huawei, gami da wasu membobin NATO.