Labarai

Buhari ya maye gurbin tsofaffin Ministoci, ya aika da sunayen wadanda aka zaɓa ga majalisa

Majalisar dattawan Najeriya ta samu bayani daga majalisar zartarwa tare da gabatar da sunayen mutane shida a matsayin wadanda za su maye gurbin ministocin da suka yi murabus domin tsayawa takarar shugaban kasa 2023.

A wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Ibrahim Lawa, ya karanta a ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace wadanda aka nada za su maye gurbin tsoffin ministocin da suka yi murabus daga mukaman su.

Wasikar ta kasance kamar haka: “A bisa sashe na 8 karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima, ina mika sunayen wadanda aka zaba a matsayin ministoci domin tabbatarwar ku.”

Wadanda aka nada sune:

Henry Ikechukwu Ikoh – Abia State

Umana Okon Umana – Akwa Ibom State

Egwumakama Joseph Nkama – Ebonyi State

Goodluck Nnana Opiah – Jihar Imo Umar

Ibrahim El-Yakub – Kano State

Ademola Adewole Adegoroye – Ondo State

Odum Odih – Jihar Ribas

Masu Alaƙa