APC ta yiwa Atiku zagon ƙasa a zaɓen 2019 – Walid Jibrin
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar People’s Democratic Party PDP, Walid Jibrin, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar All Progressives Congress APC ta yiwa dan takarar ta, Atiku Abubakar zagon kasa a zaɓen 2019.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, Jibrin ya bayyana cewa zagon kasa ne ya share fagen ganin Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya yi nasara.
Jibrin yace nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu a babban taron jam’iyyar PDP ya baiwa yan Najeriya damar kafa gwamnati ta kowa da kowa.
“Dole ne mu tuna cewa an zabi Atiku a 2019 a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP a Fatakwal, amma APC ta yi masa zagon kasa.”
Jibrin ya gaya wa yan Najeriya su tuna da “kyakkyawan aikin” Atiku a matsayin mataimakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Shugaban PDP ya dage cewa mai rike da tutar PDP shi ne mutumin da ya fi dacewa da shugabancin kasar saboda “ba dan kabila ba ne”.
Jibrin ya kara yabawa wakilan jam’iyyar, da yan jam’iyyar, ya kuma bukace su da su jajirce domin samun nasarar fita a shekara mai zuwa.