Labarai

APC Ta Baiwa Fani-Kayode Sabon Muƙami Gabanin Babban Zaɓen 2023

A karshe jam’iyyar APC mai mulki ta baiwa tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar Cif Femi Fani-Kayode sabon mukami.

Femi Fani-Kayode, wanda yayi fice wajen zage-zagen siyasa na daya daga cikin manyan ƴan siyasar kasar nan da ake mutuntawa. Ya kasance jigon babbar jam’iyyar adawa a kasar nan wato Peoples Democratic Party PDP kafin ya koma APC a bara.

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, jam’iyyar All Progressives Congress APC ta bayyana Cif Femi Fani-Kayode a matsayin Daraktan Sabbin Kafafan yada labarai na Majalisar yakin neman zaben Shugaban kasa na APC.

A jiya ne sakataren yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Abiodun Faleke ya sanyawa hannu ya kuma sanya hannu a kan nadin da jam’iyyar All Progressives Congress ta yi.

Madogararsa Labarai – All Progressive Congress Official Facebook Page

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi