Al'umma

An Sace Wayar Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo A Wurin Taro Abuja

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a wani taron da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Masu laifin sun aikata wannan aika aika ne duk da kasancewar manyan jami’an tsaro a lokacin kaddamar da wani littafi da aka rubuta don karrama tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Marigayi Solomon Lar a Abuja.

Wani tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin shi na Twitter.

Ya rubuta: “Abin mamaki ne cewa wani zai iya keta tsauraran matakan tsaro ya sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo a wajen kaddamar da littafin Marigayi Solomon Lar Book a Abuja.”

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi