An Sace Mace Ƴar Takarar Majalisar Jiha A Jos

Rundunar yan sandan jihar Filato, a ranar Alhamis, ta tabbatar da yin garkuwa da wata yar takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Matar ƴar takara, Hon. Na’anyil Magdalene Dakogol, ta kasance tana neman wakiltar mazabar Qua’an Pan ta Kudu ta a majalisar dokokin Jihar Filato a babban zaben 2023.
Kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel, wanda ya tabbatar da yin garkuwa da ƴar takarar a cikin wata sanarwa da ya fitar, yace kwamishinan yan sanda ya aike da wata tawagar masu dabara domin ceto wadda abin ya shafa.
A cewar shi, an yi garkuwa da Madalene ne a ranar da jam’iyyar ta APC ta gudanar da zaben fidda gwani.
Yace Na’anyil, wacce ita ce mace daya tilo a takarar jam’iyyar APC, na kan hanyarta ta ganawa da wakilan jam’iyyar gabanin zaben fidda gwanin da aka shirya gudanarwa a garin Kwalla na karamar hukumar Qua’an Pan na jihar, a lokacin da ta ke neman tazarce sai aka sace ta.