Labarai
An Jefe Wata Yarinya Da Duwatsu Har Ta Mutu

An jefe wata yarinya da ta kai shekaru kusan 20 da duwatsu har lahira a sanannen Round-about mai suna Eleven-Eleven da ke Calabar.
Ana kyautata zaton lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a.
An ga gawar a zagaye da wasu duwatsu da suka rage a gefen jikinta.
An ga wasu raunuka a jikinta.
Arewa Times Hausa ta kasa tantance yarinyar.
Masu tausayawa ne suka zagaye jikinta babu rai, suna kokarin tantance ta.
Motar daukar kaya tare da wasu ‘yan sanda ta isa wurin da misalin karfe 8 na safe, kuma suna shirin kwashe gawar.
Jami’ar ‘yan sanda Irene Ugbo har yanzu ba ta mayar da martani kan lamarin ba.
Zagaye na 11-11 yana gefen filin shakatawa na Millennium inda sojoji da gwamnatin jihar ke gudanar da muhimman fareti da bukukuwan Jiha.