Labarai

Aliyu ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Sokoto

Alhaji Ahmed Aliyu, tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon sakataren hukumar yan sanda, ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress APC a jihar Sokoto.

Aliyu ya samu kuri’u 1,080 daga cikin kuri’u 1,182 da aka kada a zaben fidda gwanin da yan takara shida suka fafata.

Shugaban kwamitin zaben, Alhaji Aliyu Kyari, yace Sanata Ibrahim Gobir ya samu kuri’u 36, Amb. Faruk Malami-Yabo 27, da tsohon Ministan Sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman 16 da kuri’u 23 da ba su da inganci.

Kyari ya lissafo sauran wadanda suka tsaya takara a matsayin Abubakar Abdullahi 1 da Sen. Umar Gada, 0.

NAN ta ruwaito cewa an fara atisayen ne da misalin karfe 4 na yamma a ranar Alhamis kuma ya ƙare da misalin karfe 11.40 na safiyar Juma’a.

Masu Alaƙa