Akwai Yuwar Za’a Kawo Ƙarshen Yaƙin Yukiren Ya Hanyar Tattaunawa – Amurka

Yakin da ake yi a Ukraine zai iya kawo karshe a kan teburin tattaunawa, amma dole ne yan Ukraine su iya kare kan su don karfafa matsayin su a tattaunawar zaman lafiya, in ji manyan jami’an NATO da na Amurka.
A wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka gudanar a birnin Washington, DC a ranar Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, sun ce halin da ake ciki a fagen daga zai shafi yadda tattaunawar za ta kasance nan gaba.
“Yaƙe-yaƙe ba su da tabbas,” in ji Stoltenberg ga manema labarai. “Mun sami damar yin hasashen mamayar, amma yadda wannan yakin zai samo asali, yana da matukar wahala a iya hasashen. Abin da muka sani shi ne kusan dukkanin yaƙe-yaƙe sun ƙare a wani mataki a kan teburin tattaunawa. “
Ya kara da cewa kungiyar tsaro ta NATO tana goyon bayan yancin Ukraine na kare kai yayin da ta amince da shugabancin Kyiv don yanke hukuncin nata kan tattaunawa da Moscow.