Akwai Jarirai A Cikin Mutane 22 Da Aka Kashe A Harin Coci A Ondo

Jarirai biyu na daga cikin masu ibada 22 da aka kashe a wani hari da aka kai a wata Coci a yankin kudu maso yammacin Najeriya wanda ya girgiza kasar Afirka ta Yamma, kamar yadda wani jami’in agajin gaggawa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Talata.
An kai wadanda suka mutun zuwa dakin ajiyar gawarwaki yayin da kimanin mutane 50 da suka jikkata ke cigaba da jinya a asibiti sakamakon harin da aka kai a cocin St. Francis Catholic da ke garin Owo a jihar Ondo, in ji Kadiri Olanrewaju, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya a Ondo.
Kawo yanzu dai ba a san adadin wadanda aka kashe din ba, domin wasu daga cikin wadanda aka kashen yan uwa ne suka tafi da su domin yi musu jana’iza, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.
“Wadanda ke dakin gawarwaki na asibiti ne kawai nake ba ku, ba wadanda ke cikin cocin da aka kai gida don binne su ba. Ba ni da wannan rikodin, ”in ji Olanrewaju tare da masu ba da agajin gaggawa.
Ogunmolasuyi Oluwole da Adelegbe Timileyin wadanda dukkan su ke wakiltar Owo a majalisar dokokin jihar da ta tarayya sun shaida wa Associated Press tun da farko cewa an kashe fiye da 50 a harin.
Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a Afirka mai yawan mutane miliyan 206, ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da tashe-tashen hankula a yankin arewa maso gabashin kasar daga hannun ‘yan tawaye masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama na Boko Haram da ‘ya’yanta, Lardin Islamic State West Africa.
Yanzu haka dai kasar na fama da matsalolin rashin tsaro da ake zargin ‘yan aware da ‘yan fashi da makami ne da kai hare-hare a kudancin kasar yayin da kungiyoyi masu dauke da makamai suka rika kai munanan hare-hare a yankin arewa maso yammacin kasar.