Labarai

Abinci 4 Masu Cutarwa Da Mutane Ke Ci A Kullum Da Ke Cutar Da Jikin Su

Jikinka na iya samun sauƙi wajen lalacewa ta hanyar irin abincin da kake ci a kullum amma ɗaya daga cikin matsalolin da mutane ke fuskanta a yanzu shine wasu daga cikin su ba su san nau’in abincin da ke lalata jikin su ba. A cikin wannan labarin, zan lissafta wasu daga cikin abincin da ke haifar da illa ga lafiyar ku kamar yadda wata kasida da Healthline ta wallafa ya nuna.

• Shiryayyen abinci (Fried food), da kuke ci a kullum kamar Indomie da dangin shi yana daya daga cikin abincin da ke kawo illa ga lafiyar ku domin yana dauke da isasshen adadin kuzari da mai da zai iya haifar da munanan yanayi a jikin ka. Yana ƙara yawan cholesterol na jikin ku kuma a sakamakon haka, zai iya haifar da matsalolin zuciya mai tsanani. Don haka, ya kamata ku guje wa shiryayyen abinci.

• Farin biredi wani abinci ne da ya kamata ka guji cin shi akai-akai domin bai ƙunshi adadin sinadarai masu gina jiki da ya kamata a kiyaye ba saboda duk an tace su wajen haɗa shi. Sakamakon haka, yana iya haifar da kumburi a jikin ku. Ku yawaita cin gurasar hatsi kamar burodin alkama domin yana dauke da sinadarin fiber da sauran muhimman sinadirai da jiki ke bukata.

• Sannan ya kamata a yi kokari wajen gujewa kayan shaye-shaye masu yawa domin suna iya tayar da sukarin jinin jikin ku wanda zai iya haifar da ciwon suga kuma yana haifar da babbar matsalar zuciya. Don haka, yakamata ku sha ruwa mai yawa da ƙarancin abin sha kamar lemun kwalba.

• Haka nan kuma ka nisanci abinci da ake sarrafa su nan da nan kamar dangogin indomie da sauran su domin suna dauke da abubuwan da za su iya cutar da lafiyar jikin ka, kuma ba su da sinadarai masu amfani ga jikin ka.

Masu Alaƙa