Labarai

Abin da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na Najeriya ta faɗa game da Peter Obi, Tinubu da Atiku

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo yayi takaitaccen bayani kan manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Idan dai za a iya tunawa, Peter Obi, Atiku Abubakar, Asiwaju Tinubu, da Rabiu Kwankwaso duk sun fito takarar shugaban kasa a jam’iyyun su.

Da yake zantawa da jaridar Sun a wata tattaunawa ta musamman, Alhaji Bello Bodejo yace dukkan ‘yan takarar sun yi aiki a bangarori daban-daban kuma za a tantance su ne bisa la’akari da irin ayyukan da suka yi a lokacin da suka rike ofisoshi.

A cewar shi, a matsayin shi na shugaba ya kamata a rika tunanin gobe yayin da yake rike da mukamin siyasa.

“Mun ga yadda suka jagoranci jama’a, idan kuna da mulki a yau, duk abin da kuke yi, ku tuna cewa akwai gobe.” Jaridar Sun ta ruwaito Alhaji Abdullahi Bello Bodejo yana fadar haka.

Ya kuma bayyana cewa lokaci ya yi da za a yanke shawarar wanda za a tallafa.

Masu Alaƙa