Abacha Shi Kaɗai Ya Sace Wa Najeriya Dala Biliyan $5 – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasikar dawo da kadarorin da aka kwato na kasar aka boye a kasashen ketare na duniya.
A wata makala da aka buga a jaridar Financial Times ta Landan, shugaban ya bayyana cewa an kiyasta kudaden da tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha ya sace a Najeriya, sun kai kimanin dala biliyan 5.
Shugaban wanda ya tambayi dalilin da yasa kasashen yammacin duniya suka yanke shawarar rike kudaden ya bayyana cewa kasashen Afirka na bukatar kudaden don bunkasa ababen more rayuwa.
Shugaban ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun ji dadin labarin da aka samu a wannan bazarar cewa kayayyakin tarihi 72 da aka fi sani da Benin Bronzes da ke rike da gidan adana kayan tarihi na Horniman da ke Landan suna komawa gida, shekaru 125 bayan da sojojin Birtaniya suka yi awon gaba da su.
Ya kuma kara da cewa har yanzu yunƙurin maido da dukiyoyin da aka wawashe na zama abin da ba za a iya jurewa ba, yana mai cewa “har yanzu biliyoyin daloli suna jibge a asusun bankunan ƙasashen yamma”
“An taba yin irin wannan yunƙurin maido da kadarorin Afirka da aka sace, kuma ina ganin duka biyun a matsayin wani ɓangare na gwagwarmayar dawowa Najeriya abin da ya dace namu.