Siyasa

2023: Peter Obi Ya Dakatar Da Yakin Neman Zabe, Ya Nemi Tinubu Da Atiku Su Yi Koyi Da Shi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya dakatar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023.

Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Benue a Abuja ranar Laraba.

Matakin nasa dai ya samo asali ne sakamakon halin da ‘yan kasar da ambaliyar ruwa ta shafa a wurare da dama a kasar cikin makon jiya suke ciki.

Obi ya kuma yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Atiku Abubakar da Bola Tinubu da su yi koyi da shi.

A cewar shi, idan ‘yan takarar za su iya sayen fom din bayyana ra’ayin su kan miliyoyin Naira, ya kamata su iya ba da taimako ga wadanda bala’in ya rutsa da su da suka yi hasarar kadarorin su a lokacin ambaliya.

Yace, “Ni da kaina na tsaya na ce wa jama’a ba za su kara yin kamfen ba, har sai mun samu damar ziyartar wasu wuraren, a kalla mu tausaya wa wadanda ke fama da matsalolin.

“Na zo ne domin in karbi izini na tambaye shi (Ortom) cewa ina so in ziyarci wasu yankuna a Benue kamar yadda zan yi a wata jihohi biyu.

“Ina kuma kira ga sauran ‘yan takarar shugaban kasa da su daina yakin neman zabe mu ga abin da za mu iya yi.

“Idan har za mu iya siyan fom dinmu na miliyoyin Naira, ya kamata mu samu ‘yan abin da za mu je, yanzu da mutane ke shan wahala, kuma a kalla mu tausaya musu sannan mu cigaba.”

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi