Labarai

2023: Gwamnonin PDP 5 Da Basu Halarci Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Ba

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zaben shi na zaben 2023 a Abuja a 28 ga Satumba, 2022.

An gudanar da taron ne a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja. An kuma kaddamar da wani littafi don karrama Atiku a wurin taron.

Manyan ‘yan jam’iyyar adawa da suka hada da gwamnonin jihohi sun halarci taron.

Sai dai gwamnonin PDP biyar ba su halarci muhimmin taron ba. Sun hada da:

Nyesom Wike (Rivers)

Seyi Makinde (Oyo)

Samuel Ortom (Benue)

Okezie Ikpeazu (Abia)

Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)

Rashin halartar gwamnonin a wajen taron ya nuna cewa rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP bai kare ba a yau ne aka fara yakin neman zaben 2023.

Wike da abokan shi sun dage kan cire Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa a matsayin sharadin zaman lafiya a jam’iyyar.

Duk kokarin da dan takarar shugaban kasa ya yi na kwantar da hankulan ‘ya’yan da suka ji haushi ya ci tura.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi