Labarai

2023: Gwamna Yahaya Bello ya bayar da kyautar ofishin kamfen ga Tinubu

Bayan nasarar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC da aka kammala, inda ya samu sama da rabin kuri’un wakilan jam’iyyar inda ya samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar, ya kai ziyara daban daban ga abokan hamayyar shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

A wannan karon ya je ya ga Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

A yunkurin shi na goyon bayan takarar Tinubu, Yahaya Bello ya ba shi gidan da za a yi amfani da shi a matsayin ofishin yakin neman zaben shi na shugaban kasa.

Tinubu ya je ganin sa ne a tare da tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress APC, na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole.

Tinubu ya yaba da wannan alama kuma ya yi alkawarin yi wa jam’iyyar aiki da hadin kan kasa.

Rahotanni daga CHANNELS TELEVISION na cewa ziyarar da Bola Tinubu ya kai na wani mataki ne na sasantawa da dukkan abokan hamayyar sa da suka sha kaye a zaben fidda gwani.

Masu Alaƙa