Siyasa
2023: APC Da Tinubu Basu Shiryawa Zabe Da Shugabanci Ba – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar People Democratic Party (PDP), tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba su shiryawa zabe da gudanar da mulki ba.
Atiku, a wata sanarwa da mai magana da yawun shi, Sanata Dino Melaye, ya fitar a ranar Juma’a, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi nazari sosai kan halaye da halayen mutane da jam’iyyun da ke neman shugabanci.
Yayi ikirarin cewa ana kara fitowa fili cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC na neman cigaba da rike madafun iko.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar APC ta yi amfani da farfagandar yada labarai wajen rudar da ‘yan Najeriya.