Labarai

Ɓalle Gidan Yarin Kuje: Ƴan sanda sun sake kama wani dan Boko Haram da ya gudu a Nasarawa

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce ta sake kama Hassan Hassan, wani dan ta’addar Book Haram da ya tsere daga gidan yarin Kuje kwanan nan.

Arewa Post Hausa ta tuna cewa a ranar Talata ne ƴan ta’adda suka kai hari cibiyar gyaran hali ta Kuje tare da kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da ƴan kungiyar Boko Haram da kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP).

Bayan haka, a ranar Juma’a gwamnatin tarayya ta bayyana 64 daga cikin fursunonin da ake nema ruwa a jallo da sunayen su da wasu bayanai da aka buga.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya fitar, yace an kama dan Boko Haram din da ya tsere da sanyin safiyar ranar Asabar.

Masu Alaƙa