Ƴan Sanda Sun Tabbatar Da Cafke Wani Ɗan Kasuwa A Legas Da Ake Zargin Ya Ƙona Matar Shi Har Lahira

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa wani shahararren dan kasuwa mai suna Ikechukwu Ogbonna, wanda ake zargin ya bankawa matar shi Abimbola wuta da ya kai ga mutuwar ta.
Lamarin ya samo asali ne daga wani mummunan tashin hankali na cikin gida, wanda rahotanni suka ce ya faru ne a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a gidan ma’auratan da ke unguwar Lekki a jihar inda aka ce Ogbonna, dillalin mota da aka fi sani da IVD, ya bankawa matar shi wuta cikin husuma.
Rahotanni sun bayyana cewa matar da aka ake magana ta mutu ne a wani asibiti inda aka garzaya da ita bayan gobarar ta tashi.
Sai dai ana ta rade-radin cewa wanda ake zargin ya tsere ne bayan da ya shiga shafin shi na Instagram domin mayar da martani game da mutuwar matar tasa ta hanyar wallafa wasu faifan bidiyo, inda ake zargin marigayiyar yayi masa ta’asa tare da lalata masa dukiya.
Wata sanarwa da iyalan mamaciyar suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata ta nuna cewa wanda ake zargin yana gudun ne lamarin da ya sa aka rika yada jita-jitar da ake yadawa.
“Kamar yadda kuka sani, a ranar Asabar, 15 ga Oktoba, 2022, Abimbola Martins ta rasu bayan ta yi fama da munanan raunuka a wata gobara da ta tashi a gidanta da ke Legas.
Sai dai a wani sako da kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, rundunar ta tabbatar da kama Ogbonna mai shekaru 37, tare da mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Yaba.
“An kama shi ranar Asabar, yana tare da mu. An mayar da shi sashin binciken manyan laifuka na jihar, Yaba,” inji Hundeyin.
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gurfanar da Ogbonna gaban kotu da zarar ‘yan sanda sun kammala bincikensu.