Labarai

Ƴan Sanda Sun Kashe Wasu Mutane 2 Da Ake Zargin Ƴan Bindiga Ne A Kaduna

Jami’an yan sanda a Kaduna a ranar Talata sun kashe wasu da ake zargin yan bindiga ne a yankin Birnin Gwari da ke jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, jami’an sun kuma kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu a yayin samamen.

Jalige ya ce: “A cigaba da kai farmakin da take yi da yan bindiga a Kaduna, musamman a yankin Birnin Gwari, rundunar a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, ta sake samun nasara.

“Jami’an sun kashe yan bindiga biyu tare da kwato bindigu kirar AK 47 guda biyu, yayin da wasu yan bindiga da dama suka samu raunuka.”

Masu Alaƙa