Laifuka

Ƴan Sanda Sun Cafke Malamin Jami’ar Da Ya Ci Zarafin Wata Budurwa A Cikin Faifan Biyo

A cewar wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta fitar, rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wani Malami mai suna Dokta Fred Ekpa Ayokhai da ‘yar shi da aka ɗauka a kyamara suna cin zarafin wata budurwa.

A baya an ruwaito cewa wani malami da ‘ya’yan shi sun kai farmaki gidan wata budurwa ‘yar shekara 20 da ta yi fada da diyar malamin kan wani mutum. A cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa, Agatha Akaahar, mutumin da dangin shi sun ja matar zuwa wajen gidan ta da rabin riga suka fara yi mata bulala.

A wani faifan bidiyo, an ga malamin yana yaga rigar matar da almakashi. Sun kai matar zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba, suka yi ci mutuncin ta. Matar ta roki a yi mata rahama amma babu wanda ya saurare ta.

Bidiyon ya ja hankalin hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa kuma aka fara gudanar da bincike, lamarin da ya kai ga cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin da aka gani a bidiyon.

Da yake magana da BBC News Pidgin, jami’in ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ya bayyana cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin sune; Dokta Fred Ekpa Ayokhai, malami a Jami’ar Tarayya ta Lafia a sashen nazarin tarihi da nazarin kasa da kasa da kuma ‘yar shi ‘yar shekara 18 Emmanuella Ekpa Ayokhai wadda ita ma dalibar jami’a daya ce dukkan su an kama su da hannu a cikin lamarin.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta kuma bayyana cewa, dan malamin, Godiya da sauran wadanda ake zargi da hannu wajen yiwa budurwar dukan tsiya da cin zarafi har yanzu suna hannun su. Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan ta gano daga binciken cewa wadanda ake zargin sun yiwa wacce abin ya shafa cin mutuncin ne saboda rashin jituwar da ta barke tsakanin ta da diyar malamin kan lambar wayar wani mutum.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi