Labarai

Ƴan sanda sun cafke jami’an INEC uku saboda kirkiro wurin yin rijistar katin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba a cikin Coci

Jami’an ofishin ‘yan sanda na Ijeshatedo sun kama wasu ma’aikatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) guda uku, bisa laifin hada baki da wani limamin cocin St Brigigs Catholic Church, Ijeshatedo, Legas, wajen samar da sashin rajistar katin zabe ba bisa ka’ida ba a dakin taro na cocin.

Jami’an hukumar ta INEC da suka hada da Misis Rita, Mista Ikechukwu Izuchukwu da Miss Agbokhna Ebigun, an kama su ne biyo bayan korafin da shugaban kungiyar mazauna yankin, Raji Azeem, ya kai ga ‘yan sanda kan makircin da cocin ke yi na hana wa wasu jama’a hakkinsu.

Azeem yace, mazauna wurin sun dakata a cibiyar rajistar da INEC ta amince da su, sai kawai suka gano cewa jami’an zabe sun yi sansani a zauren cocin Katolika da ke halartar mabiya cocin.

Yace, “Jami’an rajistar INEC, bisa tanadin INEC ya kamata a tsaya a 9A, Imam Thanni amma hakan bai kasance ba. Muna nan muna jiran isowar su amma da muka gano cewa ba su zo ba, sai muka damu.

Sai dai kawai mun gano cewa sun yi sansani a babban dakin taro na Cocin Katolika na St Brigigs a kan umarnin limamin cocin ya yiwa membobin cocin rajista kawai yayin da muke cikin jerin gwano. Yunkuri ne da gangan don hana mu haƙƙin mallakar katin zabe.

Cibiyar rajista ta House 9A Imam Thanni ta cigaba da zama cibiyar kada kuri’a tun 1983. Amma faston ya yanke shawarar nuna bambancin addini ta hanyar jawo jami’an zabe su yi rajistar mambobin cocin shi kawai.

Tun karfe 5 na safe ne ’yan cocin suka zo amma ba mu san shirin su ba, sai da muka kama su tare da mika su ga ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Ijeshatedo. Jami’an hukumar ta INEC da aka kama suna ta kuka da roko.

Amma hukumar ta IPO, Insifekta Shola ta bayar da belin su domin su cigaba da yin rijistar. Ya umarce su da su dawo bayan sun kammala atisayen kuma su daina gudanar da atisayen a zauren cocin su koma wurin da INEC ta amince da su.”

Wani mazaunin yankin, Omolabake Ishola, yace labarin cewa ‘yan bangar siyasa sun mamaye wurin da ake yin rajistar karya ne.
A cewar ta, da gangan kafafen yada labarai na karkatar da gaskiyar lamarin.

A cewar ta, “Babu ‘yan daba a wurin da aka yi rajista sabanin yadda wasu kafafen yada labarai ke yadawa. Maganar gaskiya dai ita ce, an yiwa jami’an hukumar zabe ta INEC ragi, inda suka yanke shawarar yin rajistar ‘yan cocin Katolika ne kawai yayin da aka bar sauran mazauna wurin.

Tun karfe 8 na safe ne muka gano cewa jami’an INEC na nan a zauren coci suna yi wa ‘yan coci rajista. Wannan bai dace ba. Daga abin da muka ji, Limamin ya sanar da cewa, ya shirya yadda jami’an zabe za su zo zauren cocin domin yin rajistar dukkan mambobinsu. Amma ya kamata mu tambayi kanmu, shin akwai wurin rajista a zauren coci? Dole ne mu kasance masu gaskiya da kanmu.”

Da yake tabbatar da kama ma’aikatan hukumar ta INEC guda uku, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an same su ne a harabar cocin suna yi wa mambobin rijista.

Ya ce, “An sanya jami’an INEC zuwa titin Imam Thanni ta House 9A domin gudanar da atisayen na yau. Duk da haka, an same su a cikin harabar cocin. Mazauna yankin sun nuna damuwa tare da sanar da ‘yan sanda. DPO Ijeshatedo ya zage damtse ya kawo jami’an INEC ofishin.”

Masu Alaƙa