Labarai

Ƴan Sanda Sun Cafke Ƴan Banga 2 Bisa Laifin Yiwa Matar Aure Fƴade

An kama wasu ƴan kungiyar ƴan banga guda biyu bisa zargin aikata laifin yiwa wata matar aure fƴade a jihar Bauchi.

Mutanen sun aikata laifin ne da bindiga a karamar hukumar Ningi da ke jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 30 ga watan Agusta, yace jami’an ƴan sanda da ke Ningi sun kama wadanda ake zargin, Lawali Sule mai shekaru 30 da Babangida Shehu mai shekaru 30 a kauyen Dogon-ruwa.

“A ranar 25 ga watan Agusta, 2022 da misalin karfe biyu na dare mutanen biyu suka hada baki a tsakanin su inda suka kai farmaki gidan wani Alhaji Gare, dukkansu dauke da bindigogin Dane-bindigo sun shiga dakin matar shi ​​wata Hadiza Alhaji (ba sunanta na gaskiya ba) inda suka tambayi mijin nata, ba ya gida lokacin. Bayan haka suka yi mata barazana da bindiga da nufin su yi mata fyade kuma ta amince saboda tsoro,” in ji sanarwar.

“An fara gudanar da bincike mai zurfi sosai. An kai matar a babban asibitin Ningi don duba lafiyar ta kuma an tabbatar da sun sadu da ita.”

“A yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin su bisa radin kan su. An kwato bindiga biyu a hannun wadanda ake zargin. CP ya bayar da umarnin a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.”

Masu Alaƙa