Labarai

Ƴan IPOB Sun Dasa Bama-Bamai A Hanyoyin South-East, 2 Daga Cikin Su Sun Jikkata – Sojoji

Wasu yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma kungiyar yan ta’adda ta Eastern Security Network (ESN) sun samu raunuka sakamakon wani bam da aka dasa a kan hanyar South-East, kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta bayyana.

Brig.-Gen. Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, yan kungiyar IPOB/ESN sun binne wasu bama-bamai a hanyoyi daban-daban a yankin Kudu maso Gabas mai fama da rikici. Yayi ikirarin cewa an yi hakan ne domin a cutar da sojojin Najeriya.

Yace yayin da suke yunkurin tserewa harin da sojojin Najeriya suka kai musu, bama-baman sun fashe tare da jikkata wasu yan kungiyar ta IPOB.

IPOB kungiya ce ta ballewa karkashin jagorancin Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu ake tsare da shi yayin da yake fuskantar tuhumar ta’addanci da sauran laifuka.

Kungiyar dai na neman ballewar yankin Kudu-maso-Gabas ne, da ma kila Kudu-maso-Kudu da ake yiwa lakabi da Jamhuriyar Biafra.

A cewar kakakin rundunar, lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, 2022, a kan hanyar Eke Ututu – Orsu a karamar hukumar Orsu ta Imo.

Nwachukwu ya bukaci mazauna yankin da su sanar da sojoji wasu wuraren da aka binne bama-baman domin a kwashe su da kuma zubar da su yadda ya kamata.

Masu Alaƙa