Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wata Ƴar Ƙasar Faransa A Kusa Da Bakassi

Ana kyautata zaton wata kungiyar yan bindiga, Black Marine, dake faretin reshen kungiyar Biafra Nations League, BNL, sun yi garkuwa da wata ma’aikaciyar mai da ake kyautata zaton yar kasar Faransa ce.

An kama wani jirgin ruwa mai sauri da ya kai ta da sauran ma’aikatan ruwa zuwa aiki, a yankin Idabato na yankin Bakassi Peninsula, yankin da aka mika wa Kamaru.

Ma’aikaciyar da ba a bayyana sunanta ba, an ce tana aiki ne a kamfanin Perenco Oil and Gas, wanda ke aiki a Rio Del Rey a mashigin tekun Guinea.

Majiyoyi sun ce jirgin ruwan wanda abin ya shafa na gudun hijira ya nufi Ndian a kudu maso yammacin Kamaru.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Alhassan Aminu ya ce, “har yanzu ina Abuja. Bari in tuntubi jami’ai na tukuna.”

Masu Alaƙa