Tsaro

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kan Ayarin Motocin Apostle Suleman, Suka Kashe Ƴan Sanda 3

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin Apostle Johnson Suleman a kan titin Benin Auchi, jihar Edo, inda suka kashe mutane bakwai da suka hada da ‘yan sanda uku.

Jaridar PUNCH ta tattaro cewa Suleman ya dawo ne daga wata tafiya kasar waje kuma yana kan hanyar shi ta zuwa jihar Edo lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kan ayarin motocin shi a kewayen yankin Auchi na jihar.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun bude wuta kan ayarin motocin Suleman, inda ake zargin sun kashe jami’an ‘yan sanda uku da wasu mutane hudu da har yanzu ba a tantance ba.

Lauyan Suleman, Samuel Amune, wanda ya tabbatar wa wakili PUNCH harin, yace malamin kiristan ya dawo ne daga wani shiri a Tanzaniya, inda ya kara da cewa ya tsallake rijiya da baya.

Yace, “Ya na dawowa daga tafiya sai ya kusa zuwa gabar tekun Auchi sai wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari. Uku daga cikin jami’an ‘yan sandan sa, da sauran su sun mutu. Ya yi tafiya kafin ya gama shirin a Tanzaniya.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi