Tsaro

Ƴan Banga Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Mai Garkuwa Da Mutane Ne, Suka Ceto Yara 2

An tattaro cewa kananan yaran da aka ce suna tsakanin shekaru 3 zuwa 4, wadanda ake zargin da kuma ‘yar aikin shi, Mrs Joy Amadi, ‘yar jihar Imo ne suka yi garkuwa da su.

Wata kungiyar ‘yan banga, OSPAC, a unguwar Ulakwo Umuselem, a karamar hukumar Etche a jihar Ribas, ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane mai suna Onyebuchi Ugo.

A cewar wani Hyacynth Nwafor, an ceto mutane biyu da aka bayyana sunayen su mai suna Savior da Joshua a karshen mako.

An tattaro cewa kananan yaran da aka ce suna tsakanin shekaru 3 zuwa 4, wadanda ake zargin da kuma ‘yar aikin s shi, Mrs Joy Amadi, ‘yar jihar Imo ne suka yi garkuwa da su.

Wadanda ake zargin sun kware wajen sace yaran da kuma sayar da su ga wadanda ba a san ko su waye ba.

An mika wadanda lamarin ya rutsa da su ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da tantance su domin samun damar gano iyayensu.

Mista Nwafor ya shawarci iyalan da ke neman ‘ya’yansu da su tuntubi hedikwatar ‘yan sandan Okehi, Okehi Etche, Jihar Ribas.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi