Wasanni
Ƴan Ƙwallo (2) Da Suka Yi “Hattrick” Da Kai A Gasar Cin Kofin Duniya

‘Yan wasa biyu sun zura kwallaye uku a raga a gasar cin kofin duniya ta FIFA.
Tomáš Skuhravý ya zura kwallaye uku a raga cikin mintuna 12 da 63 da 82 a wasan da Czechoslovakia ta doke Costa Rica da ci 4-1 a zagaye na 16 a ranar 23 ga watan Yunin 1990.
Miroslav Klose ya zura kwallaye uku a raga a cikin mintuna 20 da 25 da 70 a wasan da Jamus ta doke Saudiyya da ci 8-0 a matakin rukuni a ranar 1 ga watan Yunin 2002.